A A A A A
×

Hausa Bible 2013

Mattiyu 1

1
Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim:
2
Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yaƙub, Yaƙub ya haifi Yahuda da ʼyanʼuwansa,
3
Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu; Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Ram,
4
Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,
5
Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse,
6
Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.
7
Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abija, Abija ya haifi Asa,
8
Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yehoram, Yehoram ya haifi Azariya,
9
Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,
10
Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya,
11
Yosiya kuma ya haifi Yekoniya da ʼyanʼuwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.
12
Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon: Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,
13
Zerubbabel ya haifi Abiyud, Abiyud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor,
14
Azor ya haifi Zadok, Zadok ya haifi Akim, Akim kuma ya haifi Eliyud,
15
Eliyud ya haifi Eleyazar, Eleyazar ya haifi Mattan, Mattan ya haifi Yaƙub,
16
Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.
17
Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka, daga lokacin Ibrahim zuwa Dawuda; zuriya goma sha huɗu daga lokacin Dawuda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon, saʼan nan zuriya goma sha huɗu kuma, daga lokacin kwasa zuwa bauta a Babilon har zuwa kan Kiristi.
18
Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance: An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf, amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
19
Yusuf mijinta kuwa da yake shi mai adalci ne, bai so yǎ ba ta kunya, yǎ tone mata asiri a fili ba, ya yi tunani yǎ sake ta a ɓoye.
20
Amma bayan yanke wannan shawara, sai wani malaʼikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki, ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.
21
Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
22
Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabi cewa,
23
“Ga shi budurwa za ta yi ciki, za ta haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel,”   — wanda yake nufin, “Allah tare da mu.”
24
Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin malaʼikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa.
25
Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.
Mattiyu 1:1
Mattiyu 1:2
Mattiyu 1:3
Mattiyu 1:4
Mattiyu 1:5
Mattiyu 1:6
Mattiyu 1:7
Mattiyu 1:8
Mattiyu 1:9
Mattiyu 1:10
Mattiyu 1:11
Mattiyu 1:12
Mattiyu 1:13
Mattiyu 1:14
Mattiyu 1:15
Mattiyu 1:16
Mattiyu 1:17
Mattiyu 1:18
Mattiyu 1:19
Mattiyu 1:20
Mattiyu 1:21
Mattiyu 1:22
Mattiyu 1:23
Mattiyu 1:24
Mattiyu 1:25
Mattiyu 1 / Matt 1
Mattiyu 2 / Matt 2
Mattiyu 3 / Matt 3
Mattiyu 4 / Matt 4
Mattiyu 5 / Matt 5
Mattiyu 6 / Matt 6
Mattiyu 7 / Matt 7
Mattiyu 8 / Matt 8
Mattiyu 9 / Matt 9
Mattiyu 10 / Matt 10
Mattiyu 11 / Matt 11
Mattiyu 12 / Matt 12
Mattiyu 13 / Matt 13
Mattiyu 14 / Matt 14
Mattiyu 15 / Matt 15
Mattiyu 16 / Matt 16
Mattiyu 17 / Matt 17
Mattiyu 18 / Matt 18
Mattiyu 19 / Matt 19
Mattiyu 20 / Matt 20
Mattiyu 21 / Matt 21
Mattiyu 22 / Matt 22
Mattiyu 23 / Matt 23
Mattiyu 24 / Matt 24
Mattiyu 25 / Matt 25
Mattiyu 26 / Matt 26
Mattiyu 27 / Matt 27
Mattiyu 28 / Matt 28