English
A A A A A

2 Korintiyawa 1:1-23
1. Wasiƙa daga Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti, ɗanʼuwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korinti, tare da dukan tsarkaka a koʼina a Akayya:
2. Alheri da salama gare ku, daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.
3. Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan taʼaziyya,
4. wanda yakan yi mana taʼaziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya taʼazantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da taʼaziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.
5. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi taʼaziyyarmu ta cika har tana zuba.
6. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin taʼaziyyarku, da cetonku ne, in mun sami taʼaziyya, ai, mun same ta domin taʼaziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha.
7. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin taʼaziyyarmu.
8. ʼYanʼuwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.
9. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake ta da matattu.
10. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,
11. yayinda kuke taimakonmu ta wurin adduʼoʼinku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa adduʼoʼi masu yawa.
12. Wannan shi ne taƙamarmu: Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.
13. Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa,
14. kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.
15. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.
16. Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, saʼan nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya.
17. Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “Aʼa”?
18. Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “Aʼa” ba ce.
19. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku waʼazinsa, ai, ba “I” da “Aʼa” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.
20. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.
21. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,
22. ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yǎ tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.
23. Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korinti ba.