A A A A A

1 Korintiyawa 15:29-58
29. To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a ta da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su?
30. Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace saʼa?
31. Gaskiya, ʼyanʼuwa, ina fuskantar mutuwa kowace rana. Taƙamar da nake da ita a kanku saboda Kiristi Yesu Ubangijinmu ne ya sa na faɗa haka.
32. In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga raʼayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a ta da matattu? Ai, “Sai mu ci mu sha, da yake gobe za mu mutu.”
33. Kada fa a ruɗe ku: “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
34. Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba--na faɗi wannan ne don ku kunyata.
35. Amma wani yana iya tambaya yǎ ce, “Ta yaya ake ta da matattun? Da wane irin jiki za su tashi?”
36. Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu.
37. Saʼad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam.
38. Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta.
39. Ba dukan nama ne iri ɗaya ba: Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu.
40. Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take.
41. Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.
42. Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka ta da shi kuma ba ya ruɓewa;
43. akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma ta da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma ta da shi da ƙarfi;
44. akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma ta da shi da jikin ruhaniya. In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma.
45. Haka yake a rubuce cewa: “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”  ; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai.
46. Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya.
47. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito.
48. Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama.
49. Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.
50. Ina sanar da ku, ʼyanʼuwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba.
51. Ku saurara, in gaya muku wani asiri: Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu— 
52. farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a ta da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.
53. Gama dole mai ruɓa yǎ maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yǎ maye wa mai mutuwan nan.
54. Saʼad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, saʼan nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”
55. “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina ɗafinki?”
56. Zunubi ne yake ba wa mutuwa ɗafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko.
57. Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
58. Saboda haka, ƙaunatattu ʼyanʼuwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yǎ jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.