English
A A A A A

1 Korintiyawa 15:1-28
1. To, ʼyanʼuwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku waʼazinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai.
2. Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da waʼazin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.
3. Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi,
4. cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi,
5. cewa ya bayyana ga Bitrus, saʼan nan ga Sha Biyun.
6. Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ʼyanʼuwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci.
7. Saʼan nan ya bayyana ga Yaƙub, saʼan nan ga dukan manzannin,
8. a ƙarshe duka, ya bayyana a gare ni, kamar wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba.
9. Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah.
10. Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. Aʼa, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne.
11. To, ko ni ne, ko su ne, wannan shi ne abin da muke waʼazi, shi ne kuma abin da kuka gaskata.
12. Amma in ana waʼazi cewa Kiristi ya tashi daga matattu, yaya waɗansu a cikinku suke cewa babu tashin matattu?
13. In babu tashin matattu, to, ba a ta da Kiristi ma ba ke nan.
14. In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, waʼazinmu, da bangaskiyarku banza ne.
15. Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a ta da matattu.
16. Gama in ba a ta da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan.
17. In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan.
18. Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan.
19. In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane.
20. Amma tabbatacce, an ta da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci.
21. Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum.
22. Kamar yadda dukan mutane suka mutu cikin Adamu, haka ne dukan mutane za su rayu ma cikin Kiristi.
23. Sai dai kowa da lokacinsa: Kiristi ne nunan fari; saʼan nan saʼad da ya dawo; za a ta da waɗanda suke nasa.
24. Saʼan nan sai ƙarshen ta zo, saʼad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.
25. Gama dole yǎ yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.
26. Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.
27. Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.
28. Saʼad da ya yi haka, saʼan nan Ɗan kansa yǎ koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yǎ zama kome da kome.