A A A A A

1 Korintiyawa 14:21-40
21. A cikin Doka yana a rubuce cewa: “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji.
22. Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba.
23. Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba?
24. Amma in wani marar bi ko jahili ya shigo saʼad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yǎ gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi,
25. asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yǎ yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”
26. Me za mu ce ke nan ʼyanʼuwa? Saʼad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya.
27. In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yǎ fassara.
28. In babu mai fassara, sai mai magana yǎ yi shiru a cikin ikkilisiya, yǎ yi wa kansa magana da kuma Allah.
29. Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa.
30. In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yǎ yi shiru.
31. Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yǎ sami koyarwa da ƙarfafawa.
32. Annabawa suna da iko a kan ruhohinsu.
33. Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka,
34. ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi.
35. In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace ta yi magana a cikin ikkilisiya.
36. Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso?
37. In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yǎ gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne.
38. In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.
39. Saboda haka ʼyanʼuwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna.
40. Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.