A A A A A

1 Korintiyawa 14:1-20
1. Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci.
2. Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Hakika, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.
3. Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yǎ gina su, yǎ ƙarfafa su, yǎ kuma yi musu taʼaziyya.
4. Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina.
5. Zan so kowannenku yǎ yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.
6. To, ʼyanʼuwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayyani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba?
7. Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?
8. Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?
9. Haka yake saʼad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai.
10. Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da maʼana.
11. To, in ban gane maʼanar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni.
12. Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.
13. Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yǎ yi adduʼa a yi masa baiwar fassara.
14. Gama in na yi adduʼa da wani harshe, ruhuna ne yake adduʼa, sai dai hankalina bai amfana ba da yake ban gane ba.
15. To, me zan yi? Akwai lokatan da zan yi adduʼa da ruhuna; akwai kuma lokatan da zan yi adduʼa da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
16. A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, saʼad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?
17. Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
18. Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.
19. Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.
20. ʼYanʼuwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.