A A A A A

Galatiyawa 5:1-26
1. Saboda ʼyanci ne Kiristi ya ʼyantar da mu. Sai ku tsaya daram fa kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.
2. Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kun yarda a yi muku kaciya, Kiristi ba zai zama muku da amfani ba ko kaɗan.
3. Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yǎ kiyaye dukan Doka.
4. Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi; kun fāɗi daga alheri.
5. Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.
6. Gama a cikin Kiristi Yesu kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.
7. Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku da ba za ku yi biyayya da gaskiya ba?
8. Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.
9. “Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.”
10. Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani raʼayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.
11. ʼYanʼuwa, da a ce har yanzu ina waʼazin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan.
12. Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu bābānni!
13. Ku ʼyanʼuwana, an kira ku ga zama ʼyantattu. Amma kada ku yi amfani da ʼyancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.
14. Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya cewa: “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
15. In kun ci gaba da cizo kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.
16. Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da shaʼawace-shaʼawacen mutuntaka ba.
17. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa ƙiyaya suke yi da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.
18. Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku ƙarƙashin Doka ke nan.
19. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke: fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;
20. bautar gumaka da sihiri; ƙiyaya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,
21. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
22. Amma amfanin da Ruhu yake sa shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,
23. sauƙinkai, da kuma kamunkai. Game da irin waɗannan abubuwa babu doka.
24. Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma shaʼawace-shaʼawacensa.
25. Da yake muna rayuwa ta Ruhu, bari mu ci gaba da alʼamuranmu ta wurin Ruhu.
26. Kada mu zama masu girmankai, muna tsokana muna kuma yin ƙyashin juna.