A A A A A

Galatiyawa 4:1-31
1. Abin da nake faɗi shi ne, muddin magāji, yaro ne, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.
2. Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.
3. Haka yake, saʼad da muke yara, muna cikin bauta a ƙarƙashin ƙaʼidodin duniya.
4. Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,
5. domin yǎ fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, don mu sami cikakken matsayin ʼyaʼya.
6. Domin ku ʼyaʼya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake yin kira, “Abba, Uba.”
7. Saboda haka kai ba bawa ba ne, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
8. Dā saʼad da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda bisa ga ainihi ba alloli ba ne.
9. Amma yanzu da kuka san Allah-ko kuma a ce Allah ya san ku-ta yaya kuke sāke komawa ga ƙaʼidodi marasa ƙarfi abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu?
10. Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokatai da shekaru na musamman!
11. Ina tsoro, cewa wataƙila na yi wahala a kanku a banza!
12. Ina roƙonku ʼyanʼuwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.
13. Kamar yadda kun sani, saboda rashin lafiya ne na yi muku waʼazin bishara da farko.
14. Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce malaʼikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.
15. Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni.
16. Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
17. Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar nufi ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yǎ koma musu.
18. Yana da kyau ku yi ƙwazo, in dai manufar tana da kyau, ku kuma kasance haka kullum ba sai ina tare da ku ba.
19. Ya ku ʼyaʼyana ƙaunatattu, waɗanda nake sāke shan zafin naƙuda saboda ku, sai ran da Kiristi ya kahu a cikinku,
20. da ma a ce ina tare da ku yanzu in kuma canja muryata, domin na damu ƙwarai saboda ku!
21. Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba?
22. Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ʼyaʼya biyu maza, ɗaya ta wurin baranyar mace, ɗaya kuma ta wurin ʼyantacciyar mace.
23. Ɗansa na wajen baranyar bisa ga ƙaʼidar jiki ne; amma ɗansa na wajen ʼyantacciyar a sakamakon alkawarin ne.
24. Waɗannan alʼamura za a iya ɗaukansu a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawarai biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ʼyaʼyan da za su zama bayi: Hagar ke nan.
25. Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima, domin ita baiwa ce tare da ʼyaʼyanta.
26. Amma Urushalimar da take sama ʼyantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.
27. Domin a rubuce yake cewa: “Ki yi farin ciki, Ya ke bakararriya, wadda ba ta haihuwa ki ɓarke da murna, ki kuma ta da murya, ke da ba kya naƙuda; domin da yawa ne ʼyaʼyan macen da aka yashe, fiye da na mai miji.”
28. To, ku ʼyanʼuwa, kamar Ishaku, ku ʼyaʼyan alkawari ne.
29. A lokacin nan, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙaʼidar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.
30. Amma mene ne Nassi ya ce? “Kori baranyar da ɗanta don ɗan baranyar ba zai taɓa gādo tare da ɗa na ʼyantacciyar ba.”
31. Saboda haka, ʼyanʼuwa, mu ba ʼyaʼyan baranyar ba ne, amma na ʼyantacciyar.