English
A A A A A

Galatiyawa 1:1-24
1. Wasiƙa daga Bulus manzo-aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da Allah Uba, wanda ya ta da shi daga matattu— 
2. da kuma dukan ʼyanʼuwan da suke tare da ni, zuwa ga ikkilisiyoyi a Galatiya:
3. Alheri da salama zuwa gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi,
4. wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yǎ cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah da kuma Ubanmu,
5. a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
6. Ina mamaki yadda kuka yi saurin yashe wanda ya kira ku ta wurin alherin Kiristi, kuna juyewa ga wata bishara dabam— 
7. wadda a gaskiya ba bisharar ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi.
8. Amma ko mu, ko malaʼika daga sama ya yi waʼazin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yǎ zama laʼananne har abada!
9. Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ina ƙara cewa: In wani yana muku waʼazin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yǎ zama laʼananne har abada!
10. Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko na Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.
11. Ina so ku sani ʼyanʼuwa, cewa bisharar da nake waʼazi, ba mutum ne ya ƙago ta ba.
12. Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba ne, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.
13. Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.
14. Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin alʼadun kakannina.
15. Amma saʼad da Allah, wanda ya keɓe ni daga haihuwa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi
16. yǎ bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi waʼazinsa cikin Alʼummai, ban nemi shawarar wani mutum ba,
17. ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na yi gaggawa na tafi ƙasar Arabiya daga baya kuma na koma Damaskus.
18. Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in saba da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar.
19. Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba--sai dai Yaƙub ɗanʼuwan Ubangiji.
20. Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne.
21. Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya.
22. Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ido da ido ba tukuna.
23. Sun dai sami labari ne kawai cewa: “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana waʼazin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yǎ hallaka.”
24. Sai suka yabi Allah saboda ni.