A A A A A

2 Korintiyawa 11:1-15
1. Ina fata za ku yi haƙuri da ʼyar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri.
2. Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa tsantsa.
3. Sai dai ina tsoro kada yǎ zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwaʼu da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.
4. Gama in wani ya zo wurinku yana waʼazin wani Yesu dabam da wanda muka yi waʼazinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.
5. Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba.
6. Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.
7. Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku waʼazin bisharar Allah kyauta?
8. Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima.
9. Saʼad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ʼyanʼuwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka.
10. Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa.
11. Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!
12. Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.
13. Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, maʼaikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne.
14. Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi malaʼikan haske ne.
15. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.