English
A A A A A

2 Korintiyawa 9:9-15
9. Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.”
10. To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yǎ riɓanya shi, yǎ kuma yawaita albarkar ayyukanku na alheri.
11. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za ta zama sanadin godiya ga Allah.
12. Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.
13. Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi naʼam da bisharar Kiristi, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.
14. A cikin adduʼarsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.
15. Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!