English
A A A A A

1 Korintiyawa 11:17-34
17. Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce.
18. Da farko dai, na ji cewa saʼad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.
19. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.
20. Saʼad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba,
21. gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yǎ zauna da yunwa, wani kuma yǎ bugu.
22. Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? Aʼa, ko kaɗan!
23. Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi,
24. bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.”
25. Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk saʼad da kuke sha, don tunawa da ni.”
26. Gama a duk saʼad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yǎ dawo.
27. Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan.
28. Dole kowa yǎ bincike kansa kafin yǎ ci burodin yǎ kuma sha daga kwaf ɗin.
29. Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne.
30. Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci.
31. Amma in muka bincika kanmu, ba za a hukunta mu ba.
32. Saʼad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a hallaka mu tare da duniya.
33. Saboda haka ʼyanʼuwana, saʼad da kuka taru don ci, ku jira juna.
34. In wani yana jin yunwa, sai yǎ ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yǎ jawo hukunci. Saʼad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.