A A A A A

Romawa 9:16-33
16. Saboda haka, bai danganta ga shaʼawar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.
17. Gama Nassi ya ce wa Firʼauna: “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”
18. Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.
19. Waninku zai iya ce mini: “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?”
20. Amma wane ne kai, Ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ”
21. Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yǎ gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
22. Haka ma aikin Allah yake. Ya so yǎ nuna fushinsa yǎ kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa-waɗanda aka shirya domin hallaka?
23. Haka kuma ya so yǎ sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka— 
24. har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Alʼummai?
25. Kamar yadda ya faɗa a Hosiya: “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”
26. kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘ʼyaʼyan Allah mai rai.’ ”
27. Ishaya ya ɗaga murya game da Israʼila, ya ce: “Ko da yake yawan Israʼilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.
28. Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”
29. Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa: “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”
30. Me za mu ce ke nan? Ai, Alʼummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;
31. amma Israʼila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.
32. Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen bin ta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”
33. Kamar yadda yake a rubuce: “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”