A A A A A

Romawa 9:1-15
1. Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi-ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki— 
2. Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata.
3. Gama da so na ne, sai a laʼanta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ʼyanʼuwana, waɗannan na kabilata,
4. mutanen Israʼila. Su ne Allah ya mai da su ʼyaʼyansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawarai.
5. Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.
6. Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Israʼila ne suke Israʼila na gaske ba.
7. Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ʼyaʼyan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”
8. Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ʼyaʼyan Allah ba, aʼa, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.
9. Ga yadda aka yi alkawarin nan: “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.”
10. Ba ma haka kaɗai ba, ʼyaʼyan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.
11. Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa:
12. ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira-aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”
13. Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”
14. Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!
15. Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”