A A A A A

Romawa 8:22-39
22. Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yǎ zuwa wannan lokaci.
23. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ʼyaʼyan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.
24. Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu?
25. Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.
26. Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin adduʼa ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa.
27. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.
28. Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
29. Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yǎ zama ɗan fari cikin ʼyanʼuwa masu yawa.
30. Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31. Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
32. Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka-ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?
33. Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.
34. Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu-fiye da haka ma, shi da aka ta da zuwa rai-yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.
35. Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?
36. Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
37. Aʼa, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.
38. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko malaʼiku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki,
39. ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.