A A A A A

Romawa 8:1-21
1. Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu,
2. gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ʼyantar da ni daga Dokar Musa.
3. Gama abin da dokar ba ta iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi saʼad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yǎ zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.
4. Ya yi haka domin yǎ cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.
5. Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan shaʼawace-shawaʼacen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.
6. Ƙwallafa rai ga alʼamuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga alʼamuran Ruhu kuwa rai ne da salama;
7. hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.
8. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
9. Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.
10. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.
11. In kuwa Ruhu wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya ta da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.
12. Saboda haka ʼyanʼuwa, muna da hakki-amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba.
13. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu,
14. domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ʼyaʼyan Allah.
15. Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.”
16. Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ʼyaʼyan Allah ne.
17. In kuwa mu ʼyaʼya ne, to, mu magāda ne-magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
18. A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.
19. Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ʼyaʼyan Allah.
20. Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege
21. cewa za a ʼyantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ʼyancin ɗaukakar ʼyaʼyan Allah.