English
A A A A A

1 Korintiyawa 11:1-16
1. Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.
2. Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku.
3. To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.
4. Kowane namijin da ya yi adduʼa ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa.
5. Duk macen da ta yi adduʼa ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta-ya zama kamar an aske kanta ke nan.
6. In mace ba ta so ta rufe kanta, to, sai ta aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace ta yanke ko ta aske gashinta, to, sai ta rufe kanta.
7. Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.
8. Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.
9. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.
10. Don haka, saboda wannan, da kuma saboda malaʼiku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.
11. Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba.
12. Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.
13. Ku kanku duba mana: Ya yi kyau mace ta yi adduʼa ga Allah da kanta a buɗe?
14. Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi,
15. amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne.
16. In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata alʼada-haka ma ikkilisiyoyin Allah.