A A A A A

1 Korintiyawa 10:19-33
19. To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu?
20. Aʼa, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu.
21. Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji ku kuma ci a na aljanu.
22. Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?
23. “Ana da dama a yi kome” — sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa.
24. Kada wani yǎ kula da kansa kawai, sai dai yǎ kula da waɗansu kuma.
25. Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yǎ damu da inda abin ya fito,
26. gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”
27. In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yǎ damu da inda abin ya fito.
28. Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yǎ kasance babu laifi— 
29. ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shariʼanta ʼyancina?
30. In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
31. Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
32. Kada ku sa wani yǎ yi tuntuɓe, ko Bayahude ne, ko Bahelene ko kuma ikkilisiyar Allah— 
33. kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.