English
A A A A A

1 Korintiyawa 7:20-40
20. Ya kamata kowa yǎ kasance a matsayin da yake ciki saʼad da Allah ya kira shi.
21. Kai bawa ne saʼad da aka kira ka? Kada wannan yǎ dame ka-sai dai in kana iya samun ʼyanci, sai ka yi amfani da wannan dama.
22. Gama wanda yake bawa saʼad da Ubangiji ya kira shi, ʼyantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ʼyantacce saʼad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi.
23. Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane.
24. ʼYanʼuwa, a duk matsayin da mutum yake saʼad da aka kira shi, sai yǎ kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.
25. To, game da budurwai: Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji.
26. Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke.
27. In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure.
28. Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba ta yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.
29. ʼYanʼuwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;
30. waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne;
31. masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.
32. Zan so ku ʼyantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da alʼamuran Ubangiji-yadda zai gamshi Ubangiji.
33. Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da alʼamuran wannan duniya-yadda zai gamshi matarsa— 
34. hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da alʼamuran Ubangiji: Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da alʼamuran wannan duniya-yadda za ta gamshi mijinta.
35. Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.
36. In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yǎ yi aure, to, sai yǎ yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.
37. Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba--wannan mutum ma ya yi abin da ya dace.
38. Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.
39. Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ʼyanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji.
40. A nawa raʼayi, za ta fi jin daɗi in ta zauna haka-a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.