English
A A A A A

1 Korintiyawa 7:1-19
1. To, game da zancen da kuka rubuta: Yana da kyau mutum yǎ zauna ba aure.
2. Amma da yake fasikanci ya yawaita sosai, ya kamata kowane mutum yǎ kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.
3. Ya kamata miji yǎ cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.
4. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma.
5. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga adduʼa. Saʼan nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yǎ jarabce ku saboda rashin kamewarku.
6. Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba.
7. Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.
8. To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa: Yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake.
9. Sai dai in ba za su iya kame kansu ba, to, su yi aure, don ya fi kyau a yi aure, da shaʼawa ta sha kan mutum.
10. Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa: Kada mace ta rabu da mijinta.
11. In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yǎ saki matarsa.
12. Ga sauran kuwa (ni ne fa, ba Ubangiji ba) na ce: In wani ɗanʼuwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yǎ sake ta.
13. In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yǎ zauna tare da ita, kada ta kashe auren.
14. Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ʼyaʼyanku ba za zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.
15. Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.
16. Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?
17. Duk da haka, sai kowa yǎ kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan.
18. In an riga an yi wa mutum kaciya saʼad da aka kira shi, to, kada yǎ zama marar kaciya. In an kira mutum saʼad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya.
19. Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu.