English
A A A A A

1 Korintiyawa 5:1-13
1. Ana ba da labari cewa ana lalata a cikinku, irin da ba a ma samu a cikin masu bautar gumaka: Har mutum yana kwana da matar mahaifinsa.
2. Har ya zama muku abin taƙama! Ashe, bai kamata ku cika da baƙin ciki ku kuma daina zumunci da mutumin da yake aikata wannan ba?
3. Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku.
4. Saboda haka saʼad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.
5. Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yǎ sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo.
6. Ku daina taƙama. Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yǎ kumbura ba?
7. Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabuwar curi da aka yi babu yisti— yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu.
8. Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya.
9. Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata.
10. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yǎ zama dole ku fita daga duniya.
11. Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗanʼuwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.
12. Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ʼyan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ʼyan ikkilisiya ne za ku hukunta.
13. Allah zai yi wa waɗanda suke ba ʼyan ikkilisiya ba hukunci. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.”