A A A A A

Romawa 15:25-33
25. Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudunmawa ga tsarkaka a can.
26. Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudunmawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima.
27. Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Alʼummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya.
28. Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata.
29. Na san cewa saʼad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.
30. Ina roƙonku ʼyanʼuwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin adduʼa ga Allah saboda ni.
31. Ku yi adduʼa don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can,
32. don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku.
33. Allah na salama yǎ kasance tare da ku duka. Amin.