A A A A A

Romawa 11:19-36
19. To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”
20. Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.
21. Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.
22. Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah: tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.
23. In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.
24. Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
25. Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ʼyanʼuwa, domin kada ku ɗaga kai: Israʼila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Alʼummai masu yawa ya cika.
26. Ta haka kuwa za a ceci dukan Israʼila, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.
27. Wannan kuwa shi ne alkawarina da su saʼad da na ɗauke musu zunabansu.”
28. Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu,
29. gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.
30. Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,
31. haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.
32. Gama Allah ya ɗaure dukan mutane ga rashin biyayya don yǎ nuna jinƙai ga kowa.
33. Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34. “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yǎ ba shi shawara?”
35. “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”
36. Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.