A A A A A

Romawa 11:1-18
1. To, ina da tambaya: Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Israʼila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.
2. Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Eliya ba-yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Israʼila ya ce:
3. “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma nema su kashe ni”?
4. Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Baʼal sujada ba.”
5. Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri.
6. In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7. To, sai me? Abin da Israʼila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare,
8. kamar yadda yake a rubuce cewa: “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yǎ zuwa yau.”
9. Dawuda kuma ya ce: “Bari teburin cin abincinsu yǎ zama musu tarko, sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.
10. Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani, bayansu kuma yǎ tanƙware har abada.”
11. Har yanzu ina da tambaya: Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Alʼummai don a sa mutanen Israʼila su ji kishi.
12. Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Alʼummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!
13. Ina magana da ku ne fa Alʼummai. Tun da yake ni manzo ne ga Alʼummai, ina taƙama da aikin nan nawa,
14. da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yǎ sa in ceci waɗansunsu.
15. Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za ta zama in ba rai daga matattu ba?
16. In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.
17. In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan niʼimar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
18. kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi laʼakari da wannan: Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka.