English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 15:22-41
22. Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ʼyanʼuwa.
23. Tare da su suka aika da wannan wasiƙa: Daga manzanni da dattawa, ʼyanʼuwanku, Zuwa ga Alʼummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya: Gaisuwa.
24. Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna ta da hankalinku ta wurin abin da suka ce.
25. Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus— 
26. mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.
27. Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta.
28. Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa:
29. Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya.
30. Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.
31. Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.
32. Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ʼyanʼuwa.
33. Bayan suka yi ʼyan kwanaki a can, sai ʼyanʼuwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.
34. ***
35. Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi waʼazin maganar Ubangiji.
36. Bayan ʼyan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ʼyanʼuwa a duk garuruwan da muka yi waʼazin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.”
37. Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su,
38. amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba.
39. Suka sami saɓanin raʼayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus,
40. amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ʼyanʼuwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji.
41. Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.