A A A A A

Ayyukan Manzanni 15:1-21
1. Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ʼyanʼuwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga alʼada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”
2. Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.
3. Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Alʼummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ʼyanʼuwa suka yi murna ƙwarai.
4. Saʼad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.
5. Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Alʼummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”
6. Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar.
7. Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi, ya ce: “ʼYanʼuwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Alʼummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
8. Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
9. Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.
10. To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?
11. Aʼa! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
12. Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Alʼummai ta wurinsu.
13. Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana, ya ce: “ʼYanʼuwa, ku saurare ni.
14. Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Alʼummai su zama nasa.
15. Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce, cewa:
16. “ ‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi,
17. don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Alʼumman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’
18. da aka sani tun zamanai.
19. “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Alʼummai waɗanda suke juyowa ga Allah.
20. A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.
21. Gama Musa ya yi waʼazi a kowane birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majamiʼu kowane Asabbaci.”