A A A A A

Ayyukan Manzanni 13:26-52
26. “Ya ku ʼyanʼuwa, ʼyaʼyan Ibrahim, da ku kuma Alʼummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.
27. Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.
28. Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yǎ sa a kashe shi.
29. Saʼad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari.
30. Amma Allah ya tashe shi daga matattu,
31. kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.
32. “Muna gaya muku labari mai daɗi cewa: Abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,
33. ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin ta da Yesu daga matattu. Kamar kuma yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’
34. Gaskiyar cewa Allah ya ta da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi: “ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’
35. Haka kuma aka faɗa a wani wuri: “ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36. “Gama saʼad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.
37. Amma wanda Allah ya ta da daga matattu bai ruɓa ba.
38. “Saboda haka, ʼyanʼuwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.
39. Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba ta iya kuɓutar ba.
40. Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku:
41. “ ‘Ku duba, ku masu baʼa, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’ ”
42. Bulus da Barnabas suna fita daga majamiʼar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa.
43. Da aka sallami jamaʼa, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.
44. A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji.
45. Saʼad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.
46. Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagaɗi: suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Alʼummai.
47. Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa: “ ‘Na sa ka zama haske ga Alʼummai, domin ka kawo ceto har zuwa iyakar duniya.’ ”
48. Saʼad da Alʼummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.
49. Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin.
50. Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka ta da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.
51. Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.
52. Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.