A A A A A

Ayyukan Manzanni 13:1-25
1. A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai: Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawul.
2. Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawul domin aikin da na kira su.”
3. Saboda haka bayan suka yi azumi da adduʼa, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.
4. Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus.
5. Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majamiʼun Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.
6. Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani Bayahude mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu,
7. wanda yake maʼaikacin muƙaddas Sergiyus Faulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawul domin yana so ya ji maganar Allah.
8. Amma Elimas mai sihirin nan, (domin maʼanar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya.
9. Sai Shawul, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce,
10. “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba?
11. Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.
12. Saʼad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.
13. Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima.
14. Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majamiʼa suka zauna.
15. Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majamiʼar suka aika musu suka ce, “ʼYanʼuwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jamaʼa, sai ku yi.”
16. Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce: “Mutanen Israʼila da kuma ku Alʼummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!
17. Allahn mutanen Israʼila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar,
18. ya kuma jure da halinsu har shekara arbaʼin a cikin hamada,
19. ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kanʼana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa.
20. Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Samaʼila.
21. Saʼan nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawul ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arbaʼin.
22. Bayan an kau da Shawul, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa: ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’
23. “Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Israʼila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.
24. Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi waʼazin tuba da baftisma ga dukan mutanen Israʼila.
25. Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce: ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. Aʼa, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’