A A A A A

Ayyukan Manzanni 27:1-26
1. Saʼad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ʼyan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki.
2. Muka shiga jirgin ruwa daga Andiramitiyum wanda yake shirin tashi zuwa tasoshin da suke bakin tekun lardin Asiya, sai muka kama tafiya. Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tassalonika, yana tare da mu.
3. Washegari muka sauka a Sidon; Juliyos kuwa, cikin alheri ga Bulus, ya bar shi yǎ je wajen abokansa domin su biya masa bukatunsa.
4. Daga can kuma muka sāke kama tafiya muka zaga ta bayan tsibirin Saifurus saboda iska tana gāba da mu.
5. Saʼad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya.
6. A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki.
7. Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone.
8. Muka ci gaba a gefen gaɓar da ƙyar har muka iso wani wurin da ake kira Kyakkyawan Mafaka, kusa da garin Laseya.
9. An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su,
10. ya ce, “Mutane, ina gani tafiyarmu za ta zama da masifa ta kuma kawo babbar hasara ga jirgin ruwan da kaya, da kuma ga rayukanmu ma.”
11. Amma jarumin, a maimakon ya saurari abin da Bulus ya ce, sai ya bi shawarar matuƙi da kuma mai jirgin ruwan.
12. Da yake tashar jirgin ruwan ba ta dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma.
13. Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit.
14. Ba a jima ba, sai ga wata guguwar iska mai ƙarfin da ake kira “ʼyar arewa maso gabas,” ta buga daga tsibirin.
15. Iskar ta ci ƙarfin jirgin ruwan har ya kāsa fuskantar iskar; saboda haka muka sallama mata ta yi ta tura mu.
16. Da muka bi ta bayan wani ɗan tsibirin da ake kira Kauda, da ƙyar muka jawo ɗan ƙaramin jirgin kusa da jirgin.
17. Da mutanen suka jawo shi cikin babban jirgin ruwan, sai suka sa igiyoyi ta ƙarƙashin jirgin ruwan kanta don su ɗaɗɗaura shi. Don gudun kada a fyaɗa mu da yashin gaɓar Sirtis, sai suka saukar da ƙugiyar jirgin ruwan, suka bari aka yi ta tura jirgin haka.
18. Haka muka yi ta shan bugun guguwar hadarin nan washegari suka fara jajjefar da kayan da jirgin yake ɗauke da su a cikin teku.
19. A rana ta uku, da hannuwansu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku.
20. Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.
21. Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya miƙe tsaye a gabansu ya ce: “Mutane, da kun ji shawarata na kada ku tashi daga Kirit, da ba ku fāɗa wannan masifa da hasara ba.
22. Amma yanzu ina ƙarfafa ku ku yi ƙarfin hali, domin ba ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ruwan ne kaɗai zai hallaka.
23. Jiya da dare wani malaʼikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni
24. ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shariʼa; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’
25. Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jamaʼa, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru.
26. Duk da haka, dole a fyaɗa mu a wani tsibiri.”