A A A A A

Ayyukan Manzanni 23:16-35
16. Amma da ɗan ʼyarʼuwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus.
17. Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.”
18. Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan. Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.”
19. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?”
20. Saurayin ya ce: “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus.
21. Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arbaʼin daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.”
22. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya sallami saurayin ya kwaɓe shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka faɗa mini wannan.”
23. Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai sabaʼin da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.
24. Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.”
25. Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka:
26. Kalaudiyus Lisiyas, Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis: Gaisuwa.
27. Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne.
28. Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu.
29. Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a ɗaure shi.
30. Saʼad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka.
31. Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da daddare suka kawo shi har Antifatiris.
32. Washegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja.
33. Saʼad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus.
34. Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne,
35. sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Saʼan nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus.