English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 23:1-15
1. Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “ʼYanʼuwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yǎ zuwa yau.”
2. Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.
3. Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”
4. Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”
5. Bulus ya amsa, ya ce, “ʼYanʼuwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa: ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’ ”
6. Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar, ya ce, “ʼYanʼuwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shariʼa saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.”
7. Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu.
8. (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu malaʼiku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.)
9. Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko malaʼika ne ya yi masa magana fa?”
10. Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.
11. Washegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.”
12. Washegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus.
13. Fiye da mutane arbaʼin ne suka ƙulla wannan makirci.
14. Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus.
15. Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yǎ kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin ya iso nan.”