A A A A A

Ayyukan Manzanni 21:18-40
18. Washegari Bulus da sauranmu muka tafi domin mu ga Yaƙub, dukan dattawan kuwa suna nan.
19. Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Alʼummai ta wurin aikinsa.
20. Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Saʼan nan suka ce wa Bulus: “Ka gani ɗanʼuwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.
21. An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Alʼummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ʼyaʼyansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga alʼadunmu.
22. To, me za mu yi ke nan? Lalle za su ji cewa ka iso,
23. saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari.
24. Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.
25. Game da Alʼummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.”
26. Washegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su. Saʼan nan ya tafi haikali domin yǎ sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu.
27. Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali. Sai suka zuga taron duka, suka kama shi,
28. suna ihu suna cewa “Mutanen Israʼila ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane koʼina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri. Ban da haka ma, ya kawo Helenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.”
29. (Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.)
30. Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe. Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi.
31. Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.
32. Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
33. Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a ɗaure shi da sarƙoƙi biyu. Saʼan nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.
34. Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja.
35. Saʼad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.
36. Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”
37. Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai ya amsa, ya ce, “Ka iya Helenanci ne?
38. Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ʼyan taʼada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”
39. Bulus ya amsa, ya ce, “Ni Bayahude ne, daga Tarsus a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”
40. Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Aramayanci.: