English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 10:24-28
24. Washegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci ʼyanʼuwansa da abokansa na kusa.
25. Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin ban girma.
26. Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.”
27. Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa.
28. Sai ya ce musu: “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana Bayahude yin cuɗanya, ko ya ziyarci Baʼalʼumme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta.