A A A A A

Ayyukan Manzanni 21:13-14
13. Sai Bulus ya amsa, ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a ɗaure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
14. Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yǎ yi nufinsa.”