A A A A A

Ayyukan Manzanni 20:17-38
17. Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya.
18. Da suka iso, sai ya ce musu: “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya.
19. Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawaliʼu har da hawaye, da gwagwarmaya iri irin da na sha game da makircin Yahudawa.
20. Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku waʼazi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida.
21. Na yi shela ga Yahudawa da Helenawa cewa dole juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.
22. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba.
23. Na dai san cewa a kowane birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana.
24. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni-aikin shaida bisharar alherin Allah.
25. “Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku waʼazin mulkin Allah da zai sāke ganina.
26. Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina.
27. Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.
28. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
29. Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba.
30. Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai.
31. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.
32. “To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za ta iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake.
33. Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba.
34. Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina.
35. Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tukuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce: ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
36. Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi adduʼa.
37. Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba.
38. Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.