A A A A A

Ayyukan Manzanni 20:1-16
1. Saʼad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya.
2. Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris,
3. inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yǎ koma ta Makidoniya.
4. Sai Sofater ɗan Farrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tassalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi.
5. Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas.
6. Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai.
7. A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi washegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare.
8. Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru.
9. Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Saʼad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce.
10. Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!”
11. Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi.
12. Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma taʼazantu ƙwarai da gaske.
13. Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa.
14. Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen.
15. Washegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, washegari kuma muka iso Miletus.
16. Bulus ya yanke shawara ya wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yǎ ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri ya kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentikos.