A A A A A

Ayyukan Manzanni 19:21-40
21. Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.”
22. Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.
23. Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar.
24. Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sanaʼar nan ba.
25. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sanaʼar, ya ce, “Ku jamaʼa, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sanaʼa.
26. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan.
27. Akwai hatsari, ba kawai cewa sanaʼarmu za ta rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a koʼina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”
28. Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa: “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
29. Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya.
30. Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba.
31. Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada ya kuskura ya shiga filin nan.
32. Taron kuwa ya ruɗe: Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba.
33. Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yǎ kāre kansa a gaban mutane.
34. Amma saʼad da suka gane shi Bayahude ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa saʼa biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
35. Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, saʼan nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba ta san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba?
36. Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje.
37. Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba.
38. To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sanaʼarsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara.
39. In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa.
40. Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.”