A A A A A

Ayyukan Manzanni 19:1-20
1. Lokacin da Afollos yake a Korinti, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai,
2. sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki saʼad da kuka gaskata?” Suka amsa suka ce, “Aʼa, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.”
3. Saboda haka Bulus ya yi tambaya, ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.”
4. Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya faɗa wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.”
5. Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu.
6. Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci.
7. Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne.
8. Bulus ya shiga majamiʼa ya yi magana gabagaɗi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.
9. Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jamaʼa suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus.
10. Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da dukan ya sa dukan Yahudawa da Helenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.
11. Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus,
12. har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.
13. Waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake waʼazi, na umarce ku, ku fito.”
14. ʼYaʼya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka.
15. Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?”
16. Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.
17. Da Yahudawa da Helenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai.
18. Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu.
19. Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jamaʼa. Saʼad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimilar ta kai darakmas dubu hamsin.
20. Ta haka maganar Ubangiji ta bazu koʼina ta kuma yi ƙarfi.