English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 18:1-28
1. Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korinti.
2. A can ya sadu da wani Bayahude mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya zo ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, domin Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yǎ gan su,
3. da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamarsu, sai ya zauna ya yi aiki tare da su.
4. Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majamiʼa, yana ƙoƙari yǎ rinjayi Yahudawa da Helenawa.
5. Saʼad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin waʼazi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.
6. Amma saʼad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Alʼummai.”
7. Sai Bulus ya bar majamiʼar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titiyus Yustus, mai yi wa Allah sujada.
8. Kiribus, shugaban majamiʼa, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.
9. Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce: “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.
10. Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”
11. Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.
12. Yayinda Galliyo yake maƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu.
13. Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”
14. A daidai saʼad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku.
15. Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku-sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shariʼa kan irin waɗannan abubuwa ba.”
16. Saboda haka ya sa aka kore su daga kotun.
17. Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majamiʼa suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yǎ kula.
18. Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korinti na ʼyan kwanaki. Saʼan nan ya bar ʼyanʼuwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.
19. Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majamiʼa ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.
20. Saʼad da suka roƙe shi ya ƙara ʼyan kwanaki da su, bai yarda ba.
21. Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Saʼan nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.
22. Saʼad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya saʼan nan ya gangara zuwa Antiyok.
23. Bayan ya yi ʼyan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga koʼina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.
24. Ana cikin haka sai wani Bayahude mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.
25. An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.
26. Sai ya fara magana gabagaɗi a majamiʼa. Saʼad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.
27. Saʼad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ʼyanʼuwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata.
28. Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.