English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 17:16-34
16. Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka.
17. Saboda haka ya yi ta muhawwara a majamiʼa da Yahudawa da kuma Helenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.
18. Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana waʼazin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana waʼazin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.
19. Sai suka ɗauke shi suka kawo shi wurin taron Areyofagus, inda suka ce masa, “Ko za mu san mene ne sabon koyarwan nan ya kunsa da kake yi?
20. Kana kawo mana raʼayoyin da suke baƙo a gare mu, kuma muna so mu san mene ne suke nufi.”
21. (Duk Atenawa da baƙin da suke zama a can suna zaman kashe wando ne kawai kuma ba abin da suke yi sai dai taɗi da kuma jin sababbin raʼayoyi.)
22. Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce: “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai.
23. Gama saʼad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu: ‘GA ALLAHN DA BA A SANI BA.’ To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.
24. “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa.
25. Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome.
26. Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace alʼummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokatai bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance.
27. Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu.
28. ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
29. “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse-siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa.
30. A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a koʼina su tuba.
31. Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shariʼa da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin ta da shi daga matattu.”
32. Saʼad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jinka a kan wannan batu.”
33. Da wannan, Bulus ya bar Majalisar.
34. Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.