A A A A A

Ayyukan Manzanni 17:1-15
1. Da suka bi ta Amfifolis da Afolloniya, sai suka isa Tassalonika, inda akwai majamiʼar Yahudawa.
2. Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majamiʼar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi,
3. yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesun da nake sanar muku shi ne Kiristi.”
4. Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Helenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.
5. Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ʼyan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka ta da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron.
6. Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ʼyanʼuwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa: “Waɗannan mutanen da suke ta da fitina koʼina a duniya sun iso nan,
7. Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”
8. Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi.
9. Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki saʼan nan suka sallame su.
10. Da dare ya yi, sai ʼyanʼuwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majamiʼar Yahudawa.
11. Bereyawa kuwa sun fi Tassalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne.
12. Yahudawa da yawa suka gaskata, haka ma waɗansu manyan matan Helenawa da kuma mazan Helenawa da yawa.
13. Da Yahudawan da suke a Tassalonika suka ji cewa Bulus yana waʼazin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma ta da hankalinsu.
14. Nan da nan ʼyanʼuwa suka sa Bulus yǎ tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya.
15. Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens saʼan nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.