A A A A A

Ayyukan Manzanni 16:22-40
22. Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka.
23. Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yǎ tsare su da kyau.
24. Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.
25. Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna adduʼa suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ʼyan kurkuku kuwa suna sauraronsu.
26. Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushin ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.
27. Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, saʼad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ʼyan kurkukun sun gudu.
28. Amma Bulus ya yi ihu, ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!”
29. Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila.
30. Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yǎ daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”
31. Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto-kai da iyalinka.”
32. Saʼan nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa.
33. A wannan saʼa na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanƙe musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.
34. Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don ya gaskata da Allah-shi da dukan iyalinsa.
35. Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika maʼaikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa: “Ka saki mutanen nan.”
36. Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.”
37. Amma Bulus ya ce wa maʼaikatan: “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shariʼa ba, ko da yake mu ʼyan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? Aʼa! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.”
38. Sai maʼaikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro.
39. Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin.
40. Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da ʼyanʼuwa suka kuma ƙarfafa su. Saʼan nan suka tafi.