A A A A A

Ayyukan Manzanni 16:1-21
1. Bulus ya kai Derbe saʼan nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa Bayahudiya ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa Bahelene ne.
2. ʼYanʼuwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa.
3. Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa Bahelene ne.
4. Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye.
5. Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.
6. Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin waʼazi a lardin Asiya.
7. Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.
8. Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas.
9. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”
10. Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu waʼazin bishara.
11. Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, washegari kuma muka nufi Neyafolis.
12. Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.
13. A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin adduʼa. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana.
14. Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yardunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.
15. Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.
16. Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin adduʼa, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa-duban da take yi.
17. Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.”
18. Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita.
19. Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma.
20. Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari,
21. ta wurin koyar da alʼadun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.”