A A A A A

Ayyukan Manzanni 10:1-23
1. A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya.
2. Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma adduʼa ga Allah ba fasawa.
3. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani malaʼikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”
4. Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Malaʼikan ya ce, “Adduʼoʼinka da kyautayinka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.
5. Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus.
6. Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”
7. Saʼad da malaʼikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima.
8. Ya fada musu duk abin da ya faru saʼan nan ya aike su Yoffa.
9. Wajen tsakar rana washegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yǎ yi adduʼa.
10. Yunwa ta kama shi ya kuwa so yǎ ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa.
11. Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu.
12. Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu jan da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama.
13. Saʼan nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”
14. Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”
15. Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”
16. Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama.
17. Tun Bitrus yana cikin tunani game da maʼanar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar.
18. Suka yi sallama, suna tambaya ko Siman wanda aka sani da suna Bitrus yana zama a can.
19. Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka.
20. Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata wata, gama ni ne na aiko su.”
21. Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?”
22. Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani malaʼika mai tsarki ya faɗa masa, yǎ sa ka zo gidansa don ya ji abin da za ka faɗa.”
23. Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa. Washegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu ʼyanʼuwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi.