A A A A A

Yohanna 18:1-18
1. Da ya gama adduʼa, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.
2. To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa.
3. Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu maʼaikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai.
4. Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?”
5. Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, “Ni ne.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.)
6. Da Yesu ya ce, “Ni ne,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.
7. Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.”
8. Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne. In kuma ni ne kuke nema, sai ku bar waɗannan su tafi.”
9. Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa: “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.”
10. Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. (Sunan bawan kuwa Malkus ne.)
11. Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”
12. Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma maʼaikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka ɗaure shi
13. saʼan nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan.
14. Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yǎ mutu saboda mutane.
15. Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin,
16. Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus.
17. Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?” Bitrus ya amsa, ya ce, “Aʼa, ba na ciki.”
18. To, ana sanyi, bayi da maʼaikatan suna tsttsaye kewaye da wutan da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi.