English
A A A A A

Yohanna 13:21-38
21. Bayan ya faɗi haka, sai Yesu ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22. Sai almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake.
23. Sai ɗaya daga cikin almajiran, wanda Yesu yake ƙauna, yana zaune kusa da shi.
24. Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi.”
25. Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu ya ce, “Ubangiji, wane ne?”
26. Yesu ya amsa, ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan saʼad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.
27. Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi maza ka yi shi,”
28. amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.
29. Da yake Yahuda ne maʼaji, waɗansu sun ɗauka, Yesu yana ce masa yǎ sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yǎ ba wa matalauta wani abu.
30. Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. Da dare ne kuwa.
31. Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.
32. In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikinsa, Allah zai ɗaukaka Ɗan a cikin kansa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.
33. “ʼYaʼyana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu: Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba.
34. “Sabon umarni nake ba ku: Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.
35. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”
36. Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?” Yesu ya amsa, ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”
37. Bitrus ya yi tambaya, ya ce, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”
38. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!