English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 9:22-43
22. Duk da haka Shawul ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.
23. Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi,
24. amma Shawul ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi.
25. Amma almajiransa suka ɗauke shi da dare suka saukar da shi a cikin kwando ta taga a katanga.
26. Da ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙarin shiga cikin almajiran amma dukansu suka ji tsoronsa, ba su gaskata cewa tabbatacce shi almajiri ba ne.
27. Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawul a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi waʼazi ba tsoro a cikin sunan Yesu.
28. Saboda haka Shawul ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagaɗi a cikin sunan Ubangiji.
29. Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Helenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.
30. Saʼad da ʼyanʼuwa suka sami labarin wannan, sai suka ɗauke shi zuwa Kaisariya suka aika da shi Tarsus.
31. Saʼan nan ikkilisiya koʼina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji.
32. Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda.
33. A can ya tarar da wani mutum mai suna Eniyas, shanyayye wanda yake kwance kan gado shekara takwas.
34. Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi.
35. Duk waɗanda suke zama a Lidda da Sharon suka gan shi suka kuma juyo ga Ubangiji.
36. A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (wanda, in aka juya, shi ne Dokas ), ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta.
37. A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawanta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama.
38. Lidda yana kusa da Yoffa; saboda haka saʼad da almajirai suka ji cewa Bitrus yana a Lidda, sai suka aiki mutum biyu wurinsa su roƙe shi cewa, “In ka yarda ka zo nan da nan!”
39. Sai Bitrus ya tafi tare da su, saʼad da ya iso sai aka kai shi ɗakin saman. Duka gwauraye suka tsaya kewaye da shi, suna kuka suna nunnuna masa riguna da kuma waɗansu tufafin da Dokas ta yi yayinda take tare da su.
40. Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; saʼan nan ya durƙusa ya yi adduʼa. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune.
41. Ya kama ta a hannu ya taimake ta ta tsaya a ƙafafunta. Saʼan nan ya kira masu bi da kuma gwaurayen ya miƙa musu ita da rai.
42. Wannan ya zama sananne koʼina a Yoffa, mutane da yawa kuma suka gaskata da Ubangiji.
43. Bitrus ya zauna a Yoffa na ɗan lokaci tare da wani mai aikin fatu mai suna Siman.