A A A A A

Yohanna 13:1-20
1. Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yǎ koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.
2. Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya iza Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yǎ bashe Yesu.
3. Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah;
4. saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa.
5. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, saʼan nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul da ya ɗaura.
6. Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?”
7. Yesu ya amsa, ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”
8. Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa, ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”
9. Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!”
10. Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yǎ wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.”
11. Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.”
12. Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku?
13. Kuna ce da ni ‘Malam,’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake.
14. Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.
15. Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku.
16. Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi.
17. Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.
18. “Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’
19. “Ina faɗa muku yanzu tun kafin yǎ faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi.
20. Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”