A A A A A

Ayyukan Manzanni 9:1-21
1. Ana cikin haka, Shawul ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist
2. ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majamiʼun Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yǎ kama su a matsayin ʼyan kurkuku yǎ kai Urushalima.
3. Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.
4. Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawul, Shawul, don me kake tsananta mini?”
5. Shawul ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.”
6. “Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”
7. Mutanen da suke tafiya tare da Shawul suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba.
8. Shawul ya tashi daga ƙasa, amma saʼad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus.
9. Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba.
10. A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi, ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”
11. Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarsus mai suna Shawul, gama ga shi yana adduʼa.
12. Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don ya sāke samun ganin gari.”
13. Ananiyas ya amsa, ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.
14. Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don ya kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”
15. Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don ya kai sunana a gaban Alʼummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Israʼila.
16. Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”
17. Saʼan nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawul, sai ya ce, “Ɗanʼuwana Shawul, Ubangiji-Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan-ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”
18. Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawul, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma,
19. bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawul ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.
20. Nan take ya fara waʼazi cikin majamiʼu cewa Yesu Ɗan Allah ne.
21. Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya ta da na zaune tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don ya kai su a matsayin ʼyan kurkuku ga manyan firistoci ba?”