A A A A A

Ayyukan Manzanni 8:1-25
1. Shawul kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu koʼina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.
2. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.
3. Amma Shawul ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.
4. Waɗanda aka wartsar suka yi ta waʼazin maganar a duk inda suka tafi.
5. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.
6. Saʼad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa.
7. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.
8. Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
9. To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne,
10. dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma”
11. Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa.
12. Amma da suka gaskata da Filibus saʼad da yake waʼazin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.
13. Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus koʼina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.
14. Saʼad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna.
15. Da suka iso, sai suka yi musu adduʼa domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki,
16. domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.
17. Saʼan nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.
18. Saʼad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi,
19. ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yǎ karɓi Ruhu Mai Tsarki.”
20. Bitrus ya amsa, ya ce: “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!
21. Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.
22. Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi adduʼa ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.
23. Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma ɗaure cikin zunubi.”
24. Sai Siman ya amsa, ya ce, “Ku yi adduʼa ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”
25. Saʼad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna waʼazin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa.